Lambar girmamawa ta Nobel
January 17, 2006Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.
Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malam Abdulkadir Nura mazauni a Jihar Legas ta tarayyar Nigeria. Malamin ya na tambayar cewa,Shin ta yaya ake zaben mutanen da ake baiwa Lambar Gimamawa ta Nobel?
Amsa: Kautar Lambar girmamawa ta Nobel dai kauta ce ta dukkanin kasashen Duniya kuma ita ce kauta ta kasashen Duniya ta farko wadda ake bayar da ita duk shekara tun daga 1901, domin samun ci gaba a bangaren ilmin kimiyyar sanin karfin halicce-haliccen Duniya, wato (physics) a Turance dakuma ilimin kimiyyar sanin halayen abubuwan kasa, wato (Chemistry)a Turance, sai kuma ilimin aikin Likita wato (Medicine) a Turance, sai Bangaren rubuce-rubuce musamman ma na kasashe da kuma al’adu, sai kuma bangaren da ya shafi tabbatar da zaman lafiya akan tsarin zamantakewar al’umma.
To bayan wadannan fannoni kuma, a shekarar 1968 Bankin kasar Sweeden ya kirkiro da bada kyauta a bangaren da ya shafi ilimin kimiyyar Tattalin arziki dimin tinawa da Alfred Nobel, wato mutumin da ya aza harsashin bayar da kyautar ta Nobel.
Andai haifi Marigayi Alfred Nobel a shekarar1833 a garin Stockholm na kasar Sweeden. Nobel shine mutumin da ya kirkiro fasahar yin nakiyar nan da ta ke fasa Dutse wato (Dynamite) a Turance. Har’ila yau kuma ya gina kamfanoni da dakunan bincike na kimiyya a sama da kasashe 20 da ke a fadin wannanDuniya tamu.
Aranar 27-11-1895 ne, Nobel ya rubuta wasiyyar sa ta karshe wadda ta assasa tubalin gina bayar da wannan kyauta da ake yiwa lakabi da kyautar Nobel.
Mr. Nobel ya rasu a gidansa a garin San Remo na Kasar Italiya a ranar 10-10-1896. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka ware ranar 10 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar bikin bada kyautar Nobel domin tunawa da Marigayi Alfred Nobel.
Hanyar da ake zaben wadanda suke karbar kyautar ita ce. Kowacce shekara ana kafa wani kwamiti na musamman da zai yi aikin zakulo wadanda ake ganin sun cancanci samun wannan kyauta ta Nobel,wadanda za su iya kasancewa mutane,kungiyoyi ko kuma hukumomi. Wadannan mutane da aka nada dole ne su mika rahotonsu na wadanda suka zabo ga kwamitin a Ranar 1 ga watan Fabrairu na shekarar da za’a bayar da kyautar.
Daga nan sai kwamitin ya nemi taimakon kwararun masana wajen tantancewa da kuma fitar da wanda ya fi ko wadanda suka fi cancanta. Daganan sai su mika rahotonsu ga Hukumar da ke bayar da kyautar ta Nobel.
Ita hukumarce take zaben karshe na wanda ya ci ko wadanda suka ci nasarar samun wannan kyauta, domin a wani lokaci akan yi gamayya ne akan kyautar. Ana sanar wa da Duniya wanda ya ci wannan kyauta a watan Oktaba, kuma ana yin bikin mika kyautar ga wanda ya ci nasara a ranar 10 ga watan Disamba, wato ranar bikin tunawa da Alfred Nobel a babban dakin taro na birnin Oslo a Kasar Norway.