Lambar yabo ga mai zanen ɓatanci ga Manzon Allah
September 9, 2010Talla
Ɗan ƙasar Denmark da yayi zanen ɓatanci ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya haddasa bore a ƙasashen Musulmin Duniya Duniya, ya karɓi kyautar girmamamawa ta yancin faɗin albarkacin baki a nan Jamus. A jiya ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta miƙa wa ɗan Denmark mai zanen wato Kurt Westergaard lambar yabo ta kafafen yaɗa labarai. Westergaard mai shekaru 75 da haifuwa a shekaru biyar da suka gabata ya zana hoton Annabi Muhammadu sanye da bam a cikin rawaninsa, abinda ya jawo zanga zanga daga musulman duniya.
Mawallafi: Abdurrahaman Hassan
Edita: Umaru Aliyu