Wasu mutane uku sun lashe kyautar DW ta "THE BOBS"
May 3, 2015Talla
Wani dan gudun hijira daga kasar Siriya na daga cikin wadanda suka lashe kyautar fitattun masu fafutuka a shafin Internet na Blog da tashar DW ke bayarwa duk shekara wanda ta yi wa lakabi da "THE BOBS". Sauran wadanda suka lashe wannan kyauta sun hadar da wani dan Mexico da kuma wata 'yar kasar Bangaladash da ke fafutuka ta kafar sadarwar Internet ta hanyar yin kasada da rayuwarta domin yaki da muzgunawa da sunan addini. Alkalan gasar karo na 11 sun bayyana sunan Rafida Bonya Ahmed, wata da aka ci zarafinta a wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mijinta a kasarta Bangaladash, wadda duk da raunukan da ta samu yayin harin bata yi kasa a gwiwa wajen sanar da duniya sanadiyyar mutuwar mijin nata Avijit Roy ba.