Lambar yabo ta Nobel
December 10, 2006Muhammad Yunus ,wanda ya kafa bankin Grameen a bangladsh,bankin dake bawa talakawa marasa galihu rance,ya kasa boye farin cikinsa da samun wannan sakayya a bukin na Oslo.
Mr Yusnus ya amfani da wannan dama wajen kira ga shugabannin kasashen duniya dasu cigaba da daukan matakan yaki da talauci tsakanin jamaa,maimakon kashe biliyoyinb daloli akan yake yake,kamar na Iraki.
Ya danganta talauci da take hakkin biladama da rashin gaskiya ,a matsayin wasu daga cikin matsalolin dake haifar da rashin zaman lafiya a duniya.
A wannan bankin nasa na Grameen dai,Mr Yunus ya taimaka ingata rayuwan miliyoyin talakawa ,ta hanyar basu rance,musamman irin wanda sauran bankuna bazasu basu basu ba........
"Yace idan zaa iya yin hakan a sassa daban daban na duniya,to babu shakka zaa wayi gari wataran babu talauci a koina a duniya,talauci zai zame ne wani abu da zaa ajiyeshi domin tarihi,a gidajen tarihi,ta yadda dukkan wanda keson ganisa zai iya zuwa can ya kalla.kuma zaa iya yin haka ne daga birni zuwa birni."
Shugaban komitin bada lambar yabo ta Nobel Ole Danbolt Mjos,ya bayyana cewa an sakawa Yunus da bankinsa ne bisa kokarinsu na inganta tattalin arziki da rayuwan mutane daga tushe.
Bugu da kari yace komitin yayi wannan zabin ne da nufin rufe gibin dake tsakanin n kasashen yammaci da duniyar Musulmi,inda kasashen yammacin zasu´dauki darasi daga manufofin Yunus ,wanda ya kasance dan asalin Bangladash,daya daga cikin kasashen musulmi.
Shugaban Komitin kazalika ya jaddada cewa,daya daga cikin manufofin komitin shine yakar talauci a doron kasa.
Akan hakane Mr Yunus yace manufofin da mdd ta sanya gaba tun a shekara ta 2000,na rage talauci da rabi duniya baki daya,nanda 2015,ya samu koma baya sakamakon harin kunar bakin waken 11 ga watan satumba a Amurka da yake yaken kasar Iraki,saboda an dage hankali daga yaki da talauci zuwa yaki da ayyukan taadda.