1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Tasirin da ake gani na mulkin mallaka

April 11, 2024

Shugabannin Mulkin mallakar Jamus na ƙarshe sun bar Afrika tun sama da shekaru ɗari da suka wuce. Amma iyakokin da aka zana a Taron Berlin a tsakanin shekarar 1884 da 1885 har yanzu suna nan daram.

Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar Afirka
Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar AfirkaHoto: Comic Republic

Me Ya Sa Zirin Caprivi Ya Zama Wata Alama Ta Zana Taswirar Lokacin Mulkin Mallaka?

Har yanzu Zirin Caprivi yana ɗaya da cikin wuraren kallo na daban a kan taswirar Afrika, kuma wani yanki ne na Namibiya. Yana kama da yankin ƙasa da ya yi tsini a kan taswirar, kuma yana da layuka guda biyu a miƙe da suke da tazarar kilomita 30 a tsakaninsu da hanyoyin kurmi da kuma koguna. Babba daga cikinsu shi ne kogin Zambezi. Jami'an diflomasiyyar Turai ne suka ƙirƙire shi don su sama wa ƙasashensu yankuna ba tare da samun rikici da abokan hamayyarsu da ke maƙotaka da su a Turai ba. Kaɗan daga cikin su ne suka taɓa ziyartar wurin da suke yayyankawar, amma sun yi haka don su hana sauran ƙasashe masu mulkin mallaka cigaba da mamayar ƙasa da ake yi ta ɓangarorin Gabas Maso Yamma da Arewa Maso Kudu. 

Ta yaya aka fitar da Zirin Caprivi?

Bayan taron Berlin na shekarar 1884, an raba yankin Jamus da ke Kudu Maso Yammacin Afrika daga yankin Jamus da ke Gabashin Afrika. Abin da ya raba su shi ne keɓaɓɓen yankin Birtaniya na Bechuanal da Botswana, Arewaci da kuma kudancin Rodeshiya (Zambia da Zimbabwe a yau). Don haka, a shekarar 1890 Shugaban Jamus, Chancellor Leo von Caprivi sai ya sasanta da Birtaniya a kan wani yanki na ƙasa da zai ba wa Jamus dama ta riƙa bi ta Kudu maso Yammacin Afrika zuwa Kogin Zambezi, wanda Jamus ta san shiga cikin Afrika Ta Gabas.

Mulkin mallaka na Jamus a nahiyar AfirkaHoto: Comic Republic

Saboda wannan hanyar kasuwancin mai muhimmanci, Jamus ta amince da ikon Birtaniya a kan Zanzibar da Pemba, da suke dab da iyakar Jamus ta Gabashin Afrika, ita kuma Jamus za ta sami wani ɗan sansanin sojojin ruwa na Heligoland a tekun arewaci daga gaɓar tekun Jamus. Wannan shi ne abin da aka fi sani da yarjejeniyar Heligoland da Zanzibar ta shekarar 1890 tsakanin Birtaniya da Jamus.

Mece Ce Matsalar A Lokacin? 

A yanzu Jamus tana da daular mulkin mallaka ta huɗu mafi girma, amma kimanin kilomita 40 Gabas da inda Zirin Caprivi ya ƙare, makwararar ruwan Mosi-oa-Tunya ko daga inda Makwararar Victoria ta faro. Yanayin wannan wuri mai ban mamaki sai ya mayar da Zambezi wurin da ba ya shiguwa don haka shirin Jamus ya lalace.

Me Wannan Matsalar Tsarin Ƙasa Ta Haifar? 

Sama da al'ummomi guda shida, waɗanda suke magana da harsuna sama da goma sha biyu ne haka kwatsam suka sami kansu, a cikin kilomita kaɗan, a cikin ƙasashe 4 daban-daban.

A yayin da Zirin Caprivi ya ci gaba da zama cikin wani ƙwarya-ƙwaryan zaman lafiya a lokacin mulkin mallaka, musamman saboda Jamus tana da taƙaitattun wuraren da take da tasiri a yankin, amma hakan ya sauya, lokacin da Jamus ta rasa gundumomin mulkin mallakarta a yarjejeniyar Versailles ta shekarar 1919. Namibiya, a Kudu maso Yammacin Afrika, ta zama ƙarƙashin Afrika Ta kudu, da zummar samun ‘yancin kai daga baya. Amma hakan bai samu ba. A maimakon haka, sai Afrika Ta Kudu ta shigo da manufofinta na wariyar launin fata, ta kuma mayar da shugabannin Caprivi suka zama ‘yan amshin Shata.

Kogin VictoriaHoto: AP

Kuma daga shekarun 1960, yanayin wurin mulki da Zirin Caprivi yake ya nuna cewa fagen daga ne da kuma kai farmaki tsakanin sojojin Afrika Ta Kudu da kuma mayaƙan ƙwatar ‘yanci da suke kai hare-hare a tsakanin iyakokin ƙasa da ƙasa, da suka danganci yaƙin basasar Angola, da yaƙin kan iyaka da kuma yaƙin dajin Rodeshiya.

Rikice-rikce daban-daban guda 3 ke nan, waɗanda kuma ba su shafi mutanen da ke zaune a wurin sosai ba, amma sun shafi ƙasashen waje da suke neman su mamaye yankin. Harbe-harben bindigogi sun sassauta ne kawai a ƙarshe-ƙarshen shekarun 1990, bayan da wani yunƙurin mazauna Caprivi, na su fice daga sabuwar ƙasar Namibiya da ta sami ‘yancin kai a shekarar 1997, bai yi nasara ba.

Waɗanne Rikice-Rikicen Iyakokin Lokacin Mulkin Mallaka Ake Da Su A Tsofaffin Gundumomin Mulkin Mallkar Jamus?

A Kamaru, rikicin Bakasi ya ɓarke a shekarun 2000, tsakanin Najeriya da Kamaru a kan tsiburin Bakasi. ‘Yan asalin Najeriya sun rayu a wajen shekaru aru-aru a kan ƙasar da Kamaru take Iƙrarin tata ce bisa yarjejeniyar zamanin mulkin mallaka. Har yanzu ana samun gwabzawa lokaci zuwa lokaci, duk da hukuncin Kotun Duniya da ta yi, wanda ya ba wa Kamaru nasara.    

Haka kuma aka raba Togo, wadda ta yi iyaka da ƙasar Ghana ta yanzu, tsakanin Faransa da Birtaniya a shekarar 1919, da wata iyakar da aka ƙirƙira. Mutanen Ewe sun ƙi amincewa da wannan, waɗanda a yanzu suka sami kansu a ƙasashe guda biyu daban-daban. An shigar da "Ƙasar Togo ta Birtaniya" ko kuma Ƙasar Togo ta Yamma zuwa ƙasar Ghana a shekarar 1956 bayan kaɗa ƙuri’a. Duk da haka, yawancin yankunana Ewe sun kaɗa ƙuri’ar su zauna a ƙarƙashin ikon Majalisar Ɗinkin Duniya. Har zuwa yau wasu ƙungiyoyin Ewe suna so a ba su cin gashin kansu, ita kuma gwamnatin Ghana ta ci gaba da matsa lamba ga ‘yan gwagwarmaya ta hanyar kama su da kuma jibge sojoji a yankin.

A tanzaniya kuma, da taimakon yarjejeniyar Heligoland Zanzibar ta shekarar 1890, wadda dai ta ƙirƙiri Zirin Caprivi, akwai daɗaɗɗen rikici da Malawi a kan wa ke da iko a kan Tafkin Malawi ko Tafkin Nyasa kamar yadda mutanen Tanzaniya suke kiran sa, akwai rikici a kan a ina iyakar take. Kamar yadda yarjejeniyar ta nuna, iyakar tana kan gaɓar Tanzaniya. Ita kuma Tanzaniya ta nemi cewa ya kamata iyakar ta yi daidai da sauran iyakoki da yarjejeniya da suka danganci tafki, wato ta keta ta tsakita. Waɗannan taƙaddamomi ne guda biyu da suke kwance ba a warware su ba sai a shekarar 2011, lokacin da Malawi ta yarda da gudanar da aikin binciken mai a ɓangare tafkin da Tanzaniya take iƙrarin ta mallaka.