SiyasaAfirka
Lamuran jinkai sun sukurkuce a Sudan
November 11, 2025
Talla
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana lamuran jinkai sun gama tabarbarewa a lardin Darfur na Sudan, kuma komai ya tsaya cak, muddun aka gaza samun kudin ci gaba da ayyukan.
Halin da ake ciki
Sai dai babban jami'in kula da jinkai na majalisar ya bayyana cewa ya yi wata tattaunawa mai tasiri tare da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan, kan hanyoyin ci gaba da ayyukan agaji akasar.
Tun shekara ta 2023 fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da mayakan rundunar RSF, abin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane kana wasu milyoyi suka tsere daga gidajensu.