Ivory Coast: Komawar Laurent Gbagbo gida
June 17, 2021A shekarar 2010, an gudanar zaben shugaban kasa a Cote d'ivoire, bayan jan kafa game da batun dage zaben har sau shida tun a 2005. Kotun tsarin mulki ta tabbatar da nasarar Laurent Gbagbo a matsayin zababben shugaban kasa, amma hukumar zaben ta yi watsi da ikirarin tare da ayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben, ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan Alassane Outtara.Sai dai duk da haka Shugaba Gbagbo a lokacin ya ki ba da kai.
Karin Bayani: Gbagbo zai iya komawa gida - Ouattara
A shekarar 2011, bayan tashin tashina na tsawon watanni hudu da gazawar yunkurin sasanta juna, dakarun da ke biyayya ga Ouattara da taimakon 'yan tawayen da suka dauki makamai a yankin arewacin kasar sun sami iko da mafi yawa na kasar Ivory Coast. Faransa da Majalisar Dinkin Duniya sun jibge sojojinsu a babban birnin kasar Abidjan don hana amfani da manyan makamai a rikicin. Amma bayan kwanaki 10 da aka shafe ana barin wuta a birnin, Laurent Gbagbo ya shiga hannun dakarun sojan da ke goyon bayan Alassane Ouattara, sama da mutane 3,000 sun mutu a rikicin. A watan Mayu 2011, an rantsar da Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa, an kuma sake zabansa a 2015, kafin ya yi tazarce a shekarar 2020.