Kotu ta amince da bukatar Nnamdi Kanu
December 2, 2021Talla
Lauyoyin da ke kare shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu sun bukaci kotun da ke sauraron shari'ar a Abuja, ta umarci hukumar tsaron farin kaya bai wa Kanu din damar walwalar ganawa da mutane da abinci mai kyau tare gudanar da ibada.
Yanzu haka dai kotu ta sake dage shari'ar da ake wa Nnamdi Kanu zuwa watan Janairu na shekarar 2022, inda gwamnatin Najeriya ke zarginsa da laifuka bakwai ciki har da ta'addanci da cin amanar kasa.