Lavrov da Kerry sun tattauna kan rikicin Siriya
October 8, 2015![USA UN PK Lawrow / Kerry Treffen Nahost-Quartett in New York](https://static.dw.com/image/18752402_800.webp)
Talla
Ministan harkokin wajen Rahsa Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a kasar Siriya. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayar ta ce mutanen biyu sun yi musayar yawu kan yadda za a tuntubi juna a yakin da ake yi da kungiyar IS don hana aukuwar wani akasi musamman a sararin samaniyar kasar ta Siriya, inda jiragen yakin Rasha da Amirka ke shawagi a bama-baman da suka jefawa kan sansanonin kungiyar ta IS.