Lawyoyin Bemba sun zargi kotun ICC
January 9, 2018Lawyan da ke bai wa dan kasar Kwangon nan Jean-Pierre Bemba kariya a shari'ar da ya fuskanta a gaban kotun kasa da kasa da ke hukunta masu manyan laifuka ta ICC, ya yi kira ga kotun da ta yi watsi da shari'ar da aka yi ta matakin farko, inda ya zargi alkalan kotun da nuna bangaranci.
Shi dai Bemba wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Kwango ne kuma hamshakin dan kasuwa wanda ya kasance madugun mayaka, ya daukaka karar hukuncin da aka yanke masa na watan Yuni na 2016, inda aka yanke masa hukuncin dauri na shekaru 18 a gidan kaso sakamakon manyan laifukan da suka shafi kashe-kashen jama'a, da yi wa mata fyade da ake zargin mayakansa da yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2003.
Sai dai kuma lawyan da ke kareshi ya zargi alkalin kotun da yin watsi da shaidun da suka gabatar.