1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLebanon

An tsawaita wa'adin rundunar UNIFIL a Lebanon

August 28, 2024

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya ta UNIFIL a kasar Lebanon na tsawon shekara guda.

Hoto: MOHAMED AZAKIR/REUTERS

Lebanon: Kaucewa rikici a Gabas ta Tsakiya Kwamitin yana mai kira da a sassauta rikici bayan barkewar tashin hankali tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbullah. A cikin wani kuduri da aka amince da shi gaba daya, MDD ta yanke shawarar kara wa'adin rundunar  har zuwa 31 ga Agusta, na shekara ta 2025. Rundunar ta UNIFIL mai kunshe da dakaru sama da dubu goma da ke aiki a kudancin Lebanon tun a shekara ta  1978 domin shiga tsakanin Hizbollah da Isra'ila.  An karfafata  tun bayan rikicin kwanaki 33 tsakanin Hezbollah da Isra'ila a lokacin bazara na shekara ta   2006.