Lebanon ta haramta ayyukan Hezbollah
March 2, 2026
Talla
Haramta ayyukan Hezbollah na zuwa ne bayan da kungiyar ta harba rokoki da jirage mara matuka zuwa Isra'ila a mastayin fansar kai wa Iran hari. Harin da Isra'ila ta yi martani zuwa Beruit har ya yi ajalin mutane 31 tare da raunata sama da mutane 150 ciki har da babban jami'in leken asiri na kungiyar.
Wannan dai shi ne mataki mai zafi da gwamnatin Lebanon ta dauka a kan Hezbollah a baya-bayan nan wacce ba a taba ganin irinta ba, duk da cewa kungiyar na da wakilici a gwamnati da kuma majalisar dokoki.
Yanzu haka dakarun Isra'ila sun bayar da umarnin kwashe mutane don kaurar da su a yankunan Lebanon da dama.