1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na taya kasar Lebanon juyayi

Abdourahamane Hassane LMJ
August 5, 2020

Kasashe da dama na duniya sun yi tayin ba da agaji ga kasar Lebanon bayan fashewar wasu abubuwan wadanda suka janyo mutuwar mutane sama da 100 kana wasu sama da dubu 4000 suka samu rauni a Beirut babban birnin kasar.

Libanon | Beirut | Gewaltige Explosion am Hafen
Gine-gine sun danne mutane da dama bayan fashewar wasu abubuwa a LebanonHoto: picture-alliance/AP Photo/H. Ammar

Wannan ibtila'i dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar take cikin wani hali na rikita-rikitar siyasa kana daf da lokacin da Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta kasa da kasa za ta bayyana hukunci dangane da kisan gillar da aka yi wa tsohon firaministan kasar Rafiq al-Hariri a ranar Jumma'a mai zuwa. Wannan shi ne karon farko da aka samu fashewar abubuwan da suka janyo asarar rayuka mafi muni a kasar ta Lebanon.

Gwamnatin kasar ta ce sakaci ne na barin sinadarin Ammonium nitrate, da ake yin takin zamani da shi da kuma kera wasu abubuwan fashewa, wanda aka ajiye a wani wajen adana kayayyaki na tsawon shekaru. Mahukuntan na Lebanon, sun nunar da cewa sinadarin na Ammonium nitrate ne ya haddasa wannan barna. Kasar Holland ta ce tuni ta aike da jam'ian agaji da likitoci da 'yan sanda da jami'an kwana-kwana guda 60, yayiin da kasashen Faransa da Birtaniya da Rasha da Amirka da Jamhuriyar Chek da Poland, kowane ya nuna alhininsa tare da bayyana bayar da gudunmowarsa.

Kasashen duniya na kai gajai LebanoHoto: Reuters/IHH

A halin da ake ciki kungiyar Tarayyar Turai EU, ta ce ta aike da jam'ian kwana-kwana wadanda suka kware wajen aiki bincike domin zakulo gawarwarkin mutane da har yanzu ba a gani ba. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha alwashin taimaka wa Lebanon da tawagar masu aikin agaji 49.

Daga cikin wadanda suka raunata dai har da Jamusawa masu aiki a ofishin jakadancin kasar da ke birnin na Beirut. Ulrike Demmer Ita ce mataimakiyar kakakin gwamnatin Jamus din: ''Zan yi amfani da wannan dama domin in bayyana cewarshugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da gwamnatinta sun kadu da wannan ibtila'in, sakamkon irin hotunan bidiyon da muka gani bayan fashewar abubuwan. Muna tunawa da iyalai da suka rasa danginsu, Jamus ta bayar da tallafi ga gwamnatin Lebanon.''

Tuni da aka samu hauhawar frashin kayan abinci a kasuwanni, bayan faruwar wannan al amari. Majalisar Dinkin Duniya da ita ma ta rasa wasu ma'aikatanta sakamakon ibtila'in, ta yi gargadin cewar za a iya samun karancin garin dawa da masara da na alkama, wanda aka jigbe a tashar jiragen ruwan da fashewar abubuwan ta lalata. Kashi 80 cikin dari na abincin da ake ci Libanan akan yi odarsa ne daga waje wanda ke biyowa ta tashar jiragen ruwa, musamman ta birnin na Beirut.

Babbar tashar jirgin ruwan da ta lalace a LebanonHoto: Getty Images/AFP

Firaminista girka Kyriakos Mitsotakis, ya ce sun tura jiragen sama na agaji: ''Jirgin saman soja kirar C130 na jigilar kaya ya tashi tuni zuwa birnin Beirut tare da tawagar masu aikin ceto. Lebanon ta bukaci mu taimaka da masu aikin bicike da yin ceto."

Kididiga da hukumomi na Lebinon suka yi, ta nuna cewar kusan rabin garin Beirut ya ruguje, abin da ya janyo kusan mutane dubu 300 suka rasa matsugunansu. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce za a dade ba a samu gawarwakin wasu mutanen da harin ya rutsa da su ba. Ministan harkokin waje na Birtaniya Alok Sharma ya ce hadarin abin bacin rai ne. ''Da farko wannan wani abin jimami ne, muna tunawa da duk wadanda lamarin ya shafa, muna son taimaka wa al'ummar Beirut. Muna aiki tukuru a kan wasu jerin matakan gaggawa, wadanda za mu bayyana nan ba da jimawa ba."

Firaministan Libanon Hassan Diab ya ayyana ranar yau a matsayin ranar makokoki, yayin da sauran kasahen duniya irin Iran da Katar da Saudiya da Hadadiyar Daular Laraba da Masar da Turkiya har ma da Isara'ila wacce ba ta dasawa da Lebonon din, suka yi ma ta tayin bayar da agajin gaggawa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani