1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta 2024

April 14, 2024

Kungiyar kwallon kafa ta Bayer 04 Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta kasar Jamus yayin da ya rage makonni biyar a karkare kakar gasar ta bana.

Bundesliga - Bayer Leverkusen vs SV Werder Bremen
Hoto: EPA/CHRISTOPHER NEUNDORF

Shekaru 120 bayan kafuwarta, Bayer 04 Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga a karon farko bayan lallasa kungiyar Bremen da ci biyar da nema a filin wasa na BayArena yayin da ya rage makonni biyar a karkare kakar wasannin ta bana.

Tawagar ta Leverkusen karkashin mai horas wa Xavi Alonzo ta kawo karshen tarihi na yaya babba Bayern München da ta shafe shekaru 11 tana jan zarenta a wannan gasa tare da yi wa sauran kungiyoyi fintinkau.

Karin bayani: Wassani: Bayer Leverkusen na dab da lashe gasar Bundesliga

Baya ga kwace goruba a hannun kuturu, babban tarihin da Bayer 04 Leverkusen ta kafa shi ne a kakar wannan shekara kungiyar ta buga wasanni 43 rigis a gasannin daban-daban ba tare da yin rashin nasara ba, sannan ta bai wa kungiyar da ke biya mata a teburin Bundesliga tazarar maki 16.

A yanzu dai Leverkusen za ta mayar da hankali ne kan karamin kofin zakarun nahiyar Turai watau Europa Lig inda take neman kai wa mataki na kusa da na karshe bayan ta doke Westam Ham ta Ingila da ci biyu da nema a tsakiyar makon nan, da kuma wasan karshen na kofin kalubale na Jamus da za ta buga a ranar 25 ga watan Mayu a birnin Berlin.