1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madrid ta lashe kofin zakarun Turai

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 29, 2022

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa takwararta ta Liverpool da ci daya mai ban haushi, a wasan karshe na cin kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Turai.

UEFA Champions League | Liverpool FC I Real Madrid
Karo 14 ke nan da Real Madrid ke lashe kofin zakarun na nahiyar TuraiHoto: Kirsty Wigglesworth/AP/picture alliance

Wannan nasara dai ta bai wa Madrid din damar lashe kofin a karo na 14. Sau 17 ne dai kungiyar na samun nasarar kai wa ga wasan karshe, inda kuma ta samu nasara a wasanni 14 ta kuma yi rashin nasara a guda uku. Dan wasan Madrid din Vinicius Junior ne ya jefa kwallon a raga a mintuna na 59 da fara wasan, kwallon kuma da ta ba su nasarar lashe kofin a gaban magoya bayansu dubu 80 da suka je birnin Paris na kasar Faransa domin mara musu baya. Shi ma fitaccen dan wasan Madrid din Karim Benzema ya zura kwallo a karo na biyu sai dai ta zo da sarkakiya, abin da ya sanya aka ayyana kwallon da ya ci a matsayin satar raga. Koda yake Liverpool ta yi kokarin ganin ta samu nasara musamman ma ta hannun dan wasanta Mohamed Salah da ya rinka kai farmaki har karo uku, sai dai bai samu nasarar zura kwallo a raga ba.