Libiya da Italiya sun dauki mataki kan cinikin bayi
December 9, 2017Talla
An dai fitar da wannan sanarwar kafa kwamitin ne, bayan tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin cikin gidan Italiya Marco Minniti da Firaiministan Libiya Fayez al-Sarraj. Rahotanni na baya bayan nan sun nuna yadda a kasar Libiya ake sayar da matasa bakar fata a matsayin manoma dama cin zarafin 'yan cirani da suka fito daga kasashen arewacin Afrika masu burin zuwa nahiyar Turai. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kaduwa kan rahotannin da suka nuna yadda ake gudanar da cinikin bayi a Libiya batun da ta ce lamari ne mai tayar da hankali.