Libiya: Fatan samar da zaman lafiya
July 26, 2017Shi dai Macron ya tattauna da Firaminista kuma shugaban Libiya Fajis al-Sarraj da Janar Khalifa Haftar babban kwamandan sojoji. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani a cikin wannan rahoto.
Su dai mutanen biyu dai suna jagorantar bangarori daban daban a kasar da dole sai da su ne za a iya samun zaman lafiya a kasar mai fama da rikici. Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya sanar cewa mutanen biyu sun nuna aniyar shirya zaben majalisar dokoki a badi.
Matukar Fajis al-Sarraj da Khalifa Haftar suka cika alkawarin to taron na birni Paris zai zama wani gagarumin ci gaba. A cikin watan Mayu da ya gabata ma dai jagororin biyu sun hadu a Abu Dhabi amma sun kasa cimma daidaito kan sanarwar hadin guiwa, maimakon ko wane bangare ya bada tasa sanarwa. Ko da yake a bayan taron na Abu Dhabi sun ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki kafin watan Maris na shekarar 2018, amma barinsu kasar ke da wuya sai mummunan fada ya barke tsakanin kungiyoyin da ke mara wa ko wannensu baya.
Farfesa Andreas Dittmann na jami'ar garin Gießen da ke nan Jamus masanin siyasa ne na kasashen Larabawa da ya ce samun zaman lafiya Libya zai dogara ga hadin kan da shugabannin biyu za su ba juna.
Ya ce: "Ya kamata 'yan Libiya sun san cewa su kadai ba za su iya yin aikin sake gina kasar ba sai da taimakon kasashen ketare, domin rikicin kasar ya zama na yankin baki daya, inda wasu mayaka irin na IS ke samun angizo. Na biyu kuma shi ne aiki sake gina kasar zai yiwu ne idan shugabannin biyu suka ba wa juna hadin kai. Kuma ma wannan shi ne matsayin kasashen yamma wato hadin kan cikin gida a Libiya a matsayin sharadin farko na sauran abubuwan da za su biyo baya."
Tun bayan yakin basasan shekarr 2014 ake da gwamnatoci biyu a Libiya daya a Triplois dayar kuma a Tobruk da ke gabashin kasar. A shekarar 2015 bangarorin biyu sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya da ta tnadi kafa gwamnatin hadin kai karkashin jagorancin Fajis al-Sarraj, sai dai ba ta samu goyon bayan dukkan 'yan siyasar gabashin kasar ba, musamman ma na kurkusa da Janar Khalifa Haftar.
To ko yanzu za a samu wannan hadin kai da zai kai ga shirya zabe a badin? Farfesa Andreas Dittmann na jami'ar Gießen ya yi karin haske.
Ya ce: "Bisa al'adar siyasar Libya ba a taba yin zabe na gaskiya da adalci ba. Wannan shi ne bambamcinta da kasashen irinsu Tunisiya ko Masar. Ba a taba wani mulki na demokaradiyya a kasar ba."
Matukar aka yi nasarar kawar da wannan al'ada sakamakon taron na birnin Paris, to ke nan Macron zai kasance sahun gaba a matsayin mai shiga tsakani na waje da ya yi nasarar sasanta bangarorin da ke rikici da juna a Libiya.