An kori dakarun Haftar daga sansanin sojin sama
May 18, 2020Talla
Col. Mohammed Gnounou da ke magana da yawun gwamnatin kasar ta Libiya ne ya tabbatar da wannan nasara ta karbe sansanin sojin sama na al-waitya da ke kudu maso yammacin kasar. Tuni Firai Ministan kasar ya sanar da cewa sannu a hankali za su karbe dukka garuruwan da ma yankunan da ke hannun dakarun Janar Haftar din.
Za a iya cewa wannan wani babban komabaya ne ga Khalifa Haftar da ma dakarunsa da suka kwashe sama da shekara suna ikirarin sai sun karbe ikon birnin Tripoli.