Libiya: Masunta sun gano gawarwaki a Teku
April 18, 2017Talla
Kwamandan kula da tsaron sashin cikin gida a Libiya Ahmaida Khalifa Amsalam ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa an binne gawarwakin da masuntan suka gano cikin ruwa a rami guda ciki kuwa har da mata hudu.
A tun bayan juyin juya halin da ya kifar da mulkin tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, kasar ta zamo kofa ga bakin haure sama da dubu 150 a duk shekara suna silalewa ta ruwa zuwa nahiyar Turai.