Za a kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Libiya
February 1, 2021Talla
A taron za a fara da sauraren 'yan takara 45 da za su kara a zaben shugabannin da suka hada da tawagar mutum uku da za su shugabanci kasar da kuma Firaminista da zai ja ragamar mulkin kasar har zuwa watan Disamban bana kafin a gudanar da zaben gama gari.
Da take jawabi ga wakilai a taron, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Libiya Stephanie Williams ta yi kira ga bangarorin biyu, a matsayinsu na wakilan al'umma da su yi aiki tare domin fitar da kasar daga halin da ta shiga.
Kasar ta Libiya na cikin wani hali na rashin tabbas tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011.