Libiya ta ayyana samun 'yancin kai
October 23, 2011Ayyana samun 'yancin ya zo ne a yayin gudanar da shagulgula a birnin Benghazi dake yankin gabashin ƙasar, inda anan ne boren nuna adawa da mulkin Gadhafin ya samo asali. Hakanan birnin ne ke zama cibiyar majalisar wucin gadin ƙasar a Libiya. Ayyana samun 'yanci shi ne matakin farko game shirin gudanar da zaɓuka a ƙasar ta Libiya, bayan watannin da aka yi ana zubar da jini a ƙasar. A jawabin daya yi lokacin bukukuwan, shugaban majalisar wucin gadin ƙasar ta Libiyas Mustafa Abdel Jalel, ya bayyana cewar duk wata gwamnatin da za'a samar nan gaba a Libiya za ta rungumi tsarin musulunci ne a matsayin tushen dokokin ta. A ranar Alhamis da ta gabata ce 'yan tawayen Libiyar dake samun tallafin sojojin ƙawancen tsaron NATO suka yi galaba akan dakarun Gadhafi bayan cafke shi a mahaifarsa dake garin Sirte, inda kuma ya mutu jim kaɗan bayan hakan. Wani binciken da jami'an kula da lafiya suka gudanar, a yanzu ya tabbatar da cewar Gadhafi ya mutu ne sakamakon raunin daya samu daga harbin bindigar da aka yi masa a kai. Tunda farko jami'an gwamnatin wucin gadi suka ce ya mutu ne a lokacin musayar wuta, amma wani hoton bidiyon da aka fitar ya nunar da cewar cafkeshin da aka yi ya sa wasu am,annar cewar da gangan ne aka harbe shi.
Mawallafi: Umar Saleh umar
Edita : Zainab Mohammed Abubakar