1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Tsagaita wuta ta dindindin

Abdullahi Tanko Bala AAI
January 22, 2020

Kudiri mai karfi da ya fito daga taron Berlin don sulhunta rikicin Libiya shi ne cewa, tilas ne a samu tsagaita wuta ta dindindin. 

Yadda ake ta barin wuta a rikicin Libiya
Yadda ake ta barin wuta a rikicin LibiyaHoto: AFP/M. Turkia

 

Har yanzu an katse yankunan da ke kewaye da Tripoli wadanda ke karkashin ikon gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita daga sauran yankunan kasar. Firaminista Fayez al Sarraj yana takun saka da Khalifa Haftar wanda ya toshe fitar da mai daga yankin. Sai dai 'yan kasar suna da fatan za a sami masalaha.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya a taron Berlin Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Wasu da dama dai na son ganin shugabannin Afirka sun kasance masu karfin fada a ji, wajen sasanta rikicin, kamar yadda wannan mutumin a Nijar wadda ke makwabtaka da Libiya yake fatan gani. Yana mai cewa bai san dalilin da ya sa za a je Berlin a tattauna  warware rikicin Libiya ba, ba tare da an shigar da kasashen Chadi da kuma Nijar ba.

"Ya ce ya kamata shugabannin Afirka su hada kai su amince da Libiya a matsayin 'yar uwarsu, su kuma taimaka mata. Su hada kai da LIbiya, wajibi ne su yi hakan domin gano bakin zaren warware matsalolin da suka addabi kasar."

Sanarwa ta baya-bayan nan ta fuskar siyasa da ta fito daga shugabannin na Afirka, kamar na kasar Congo Denis Sassou-Nguesso inda ya baiyana cewa Libiya kasar Afirka ce hasali ma kuma wadda aka kafa kungiyar hadin kan Afirka da ita kamar yadda Ministan harkokin wajen kasar Jean-Claude Sassou-Nguesso Gakasso ya shaida wa wata mujallar Faransa. Sai dai abin takaici shi ne ba a daukar shawarar Afirka idan ana maganar sulhunta rikicin Libiya. Amma magana ta gaskiya ita ce dole ne a yi taron sasantawa kuma wajibi ne 'yan Libiya su hada kansu su zauna teburin sulhu.

Irin makaman da ake shigo wa da su LibiyaHoto: Imao-Images/Xinhua/A. Salahuddien

Acheick Ibn Oumar mai baiwa shugaban Chadi Idriss Deby shawara kan al'amuran diflomasiyya ya yi bayani da cewa 
"Yace wadanda ke da ruwa da tsaki a Libiya sun fi sauraron wadanda ke basu makaman yaki amma ba masu basu shawara ba. Haka duniya ta ke. Amma muna jin cewa lokaci zai zo ga Afirka da zai hada kan kowa wajen shawarwari, inda kuma za a saurari makwabtan Libiya kai tsaye."

Taron sasantawar da aka yi a Berlin ya zama dole ne, saboda yadda mayakan Haftar suka rika dannawa don kai wa ga Tripoli a cewar wani manazarci, Fonteh Akum. Sai dai abun sa ido a gani shi ne inda zai karkata walau ga Rasha ko kuma Turkiyya, kasashe biyu da ke taka rawa a kasar ta Libiya. 


"Ya ce mun ga yadda ake nuna karfin tasiri a tsakanin manyan kasashe kamar Rasha da Turkiyya, za su iya yin tasiri  a kan yadda Khalifa Haftar zai bada hadin kai ga Firaminista Fayez al Sarraj."


A waje guda dai shugaban kasar Kongo Denis Sassaou-Nguesso ya gayyaci kasashen Afirka wani taron koli a Brazzavile a ranar 30 ga wannan watan yayin da a daya bangaren shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ke shirin karbar ragamar shugabancin kungiyar tarrayar Afirka daga shugaba Al Sisi na Masar, cikin 'yan kwanaki masu zuwa. Ko za a sami sauyin da kungiyar tarayyar Afirka za ta nuna tasiri a karkashin jagorancin Ramaphosa, lokaci ne zai nuna.

Shugaban kasar Kongo Denis Sassaou-Nguesso a taron BerlinHoto: Reuters/M. Tantussi