1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya za ta tattauna da 'yan tawaye

July 12, 2011

Gwamnatin Libiya ta sanar da cewa a shirye ta ke ta yi sulhu da yan tawaye da kuma ƙungiyar tsaro ta NATO

Muammar GaddafiHoto: dapd

Frministan ƙasar Libiya Baghdadi al Mahamoudi ya sanar da cewa mai yiwa a kai ga yin tattaunawar neman sulhu, tsakanin gwamnati da yan tawaye da kuma ƙungiyar tsaro ta NATO ba tare da halartar Kanal Muammar Gaddafi ba a shawarwarin.

Al Mahamoudi wanda ya ce a shirye suke su tattauna ba tare da giciya wani sharaɗi ba ya ce za a baje komai a ƙasa domin samun mafita ga rikicin. A cikin wata fira da yayi da shugaban ƙasar Rasha ta waya tarho, shugaban Amurka Barack Obama ya shaidda masa cewa suna goyon bayan tattaunawar idan har Kanal Gaddafin zai sauka daga mulkin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu