1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Libya:Yan takara 98 ke neman shugaban kasa

Abdoulaye Mamane Amadou
November 23, 2021

A yayin da ake shirin zaben shugabancin kasa a Libiya, hukumar zaben kasar ta ce 'yan takara 98 ne suka nuna sha'ar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na watan gobe

Libyen Verfassung Abstimmung 20.02.2014
Hoto: Reuters

Tuni hukumar zaben ta ce nan da zuwa kwanaki 12 take sa ran fitar da jerin sunayen wadanda suka cika ka'idojin takara, kafin daga bisani ta mika takardun a gaban kotu don kara tantancesu, tare da duba daidaitonsu da dokokin zaben Libiya.

Akwai mata biyu da suka nuna sha'awar tsayawa takara a zaben shugabancin kasar, baya ga wasu masu karfin fada aji da suka fito tun daga farko, ciki har da dan tsohon shugaban kasar ta Libiya Seif al-Islam Kadhafi da Khalifa Haftar da shugaban gwammatin rikon kwarya Abdelhamid Dbeibah.

Kawo yanzu mutane miliyan daya da rabi ne daga cikin mutum fiye da miliyan biyu da suka cancanci zabe suka karbi katinsu a cewar hukumar zaben kasar mai zaman kanta.