1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Libya: Jamus na son China da Rasha su fito da gaskiya

September 26, 2020

Jamus na kira ga kasashen China da Rasha da su daure su fitar da rahoton sakamakon binciken dokar hana safarar makamai zuwa Libya.

Deutschland Merkel PK
Hoto: Getty Images/AFP/M. Kappeler

Guenter Sautter jakadan Jamus a Majalisar Dinkin Duniya ya ce kasarsa na son kwamitin sulhu ya zauna domin yin nazari kan wannan rohoto, domin a sanar da duniya yadda wasu mutane suke kai makamai kasar Libya. 

Jamus ta ce akwai bukatar a zargi wadanda ke aikata wannan barna kuma idan an kama su dumumu to ya kamata a kunyata su. To sai dai a gefe guda kasashen Rasha da China sun ci gaba da nuna adawa da matakin, inda wasu majiyoyi na sirri ke nuna yadda kasashen ke son kar a wallafa rahoton.