Libya: Khalifa Haftar ya bukaci kayan aiki
September 29, 2017Talla
Haftar ya yi wadannan kalamai ne yayin wata hira da aka yi da shi wadda aka wallafa a wannan juma'ar bayan da ya gana da hukumomin Italiya da na Faransa. Marshal Haftar ya ce ya na da tsari wanda zai bada damar tattaunawa da kasashe makwabtan Libya inda bakin hauren ke fitowa.
Sai dai kuma Haftar ya ce idan har kasashen Turai na bukatar a kawo karshen kwarar bakin haure, sai sun taimaka an kawo karshen haramcin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kasar ta Libya na shigar da duk wasu kayayyakin da suka shafi harkokin soja a kasar.