1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya: Shekaru 10 bayan kifar da Ghaddafi

Abdullahi Tanko Bala
February 17, 2021

Al'ummar kasar Libya a wannan Laraba suna bukukuwan cika shekaru 10 da juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin shugaban kasar mafi dadewa a karagar mulki Muammar Gaddafi abin da kuma ya jefa kasar cikin rudani.

Libyen Demo zum Jahrestag der libyschen Revolution
'Yan Libya na muranar zagayowar Juyin juya haliHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

A yammacin kasar Libya jama'a sun taru a wani dandali domin bukukuwa tare da wasan wuta da faretin soji yayin da a gabashin kasar wadda ke da gwamnati ta daban tsawon shekaru hudu a yanzu yanayin ya kasance na nuna alhini.

A jajiberen bukukuwan, birane da dama a yammacin Libya ciki har da Tripoli babban birnin kasar sun gudanar da faretin soji da wasan wuta.

Gabanin bukukuwan jakadan Majalisar Dinkin Duniya Jan Kubis ya gana da shugabannin Libyan a ziyararsa ta farko zuwa kasar ta gabashin Afirka tun bayan nada shi akan matsayin.

Kubis ya jaddada muhimmancin mika mulki cikin ruwan sanyi bayan tattaunawar sulhu da aka cimma nasara a Switzerland.