1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Libya ta saki wasu mayaka

April 1, 2021

Mahukunta a yammacin Libya sun saki mayakan rundunar gabashin kasar su 120, a wani yunkurin sasanci na shirin Majalisar Dinkin Duniya don kawo karshen rikici na tsawon shekaru.

Libyen | General Chalifa Haftar
Hoto: Costas Baltas/Reuters

Mayakan da aka kama a watan Afrilun shekarar 2019 a kusa da garin Zawiya da ke yammacin kasar na biyayya ne ga mayakan Khalifa Haftar wadanda suka kaddamar da farmaki don kwace birnin Tripoli daga gwamnatin hadaka a shekarar.

A jawabinsa yayin sakin mayakan mataimakin shugaban kasar a sabuwar gwamnatin Libya Abdallah al-Lafi ya yi maraba da wannan ci gaban tare da yin kira kan sake hada kai da yin sulhu da kuma aje dukkan wani bambamci ko gaba da ke tsakani. Libya dai ta shiga cikin rikice-rikice tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Moammar Ghaddafi a shekarar 2011.