Lieberman ya yi murabus
December 14, 2012Talla
Lieberman mai shekaru 54 ya ce ko da yake bai aikata wani laifi ba, to amma zai sauka daga muƙaminsa na ministan harkokin waje da kuma na mataimakin Firaminista . A jiya Alhamis ma'aikatar shari'ar ƙasar ta Isra'ila ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin cin hanci a da kuma halasta kuɗin haram.Ana dai rashin sanin tabbas game da tasirin da hakan zai yi akan zaɓen majalisar dokoki da zai gudana a watan Janairu.
A watan Nuwamban da ya gabata ne dai, jam'iyyar Liebermann mai matsanancin ra'ayin jari hujja da jam'iyyar firaiminista Benjamin Netanyahu ta Likud suka ba ba da sanarwar ƙulla ƙawance a zaɓen na watan Janairu.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi