1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitan Japan ya mutu a harin ta'addanci

Ramatu Garba Baba
December 4, 2019

Tetsu Nakamura Likita ne da yayi fice a kasar Afghanistan a sakamakon jajircewa da sadaukar da rayuwarsa da yayi don ganin ya ceto rayuwar dubban al'umma musanman marasa galihu da ke rayuwa a tsakiyar rikici.

Afghanistan  Tetsu Nakamura
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sadeq

Sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta Afghanistan ta fitar, ta nuna takaici kan mutuwar babban jami'in da asalin kasar Japan da kuma wasu mutum biyar da suka halaka a harin na wannan Laraba. Nakamura shi ne shigaban kungiyar agaji ta Japan da ke da reshe a Afghanistan, ya kwashi fiye da shekaru talatin yana tallafawa majinyata a kasashen Afghanistan da Pakistan kafin ya gamu da ajalinsa.

Mai magana da yawun shugaban kasar Sediq Seddiqi, ya baiyana likitan dan shekaru 73 da haihuwa, a matsayin jarumi kuma aminin Afghanistan da ya jefa rayuwarsa cikin hadari don ganin ya ceto rayukan al'umma musanman marasa galihu a kasar da ke ci gaba da fama da tashe-tashen hankula.


Kungiyar Taliban da ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a kasar, ta nesanta kanta da harin, inda ta ce fadan da take yi bai shafi kungiyyoyi agaji ba saboda haka bata da hannu a kisan Nakamura. An dai kai hari kan tawagar likitan inda shi da wasu masu aikin kare shi da kuma direbansa suka halaka.