1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci sun fara yajin aiki a Najeriya

June 15, 2020

Yayin da ake kokarin shawo kan cutar corona, likitoci sun dakatar da aiki don neman biyan bukata daga mahukunta musamman a wannan lokaci da annobar ke ci gaba da barazana.

Massenproteste in Nigeria
Hoto: dapd

Likitoci a Najeriya, sun tsunduma yajin aiki a yau Litinin saboda kokawar da suke yi kan rashin cika sharuda da suka bai wa hukumomin kasar game da albashinsu da kuma karancin kayan kare kai daga kamuwa da cutar COVID-19 lokacin da suke aiki.

Najeriyar da ke da al'uma miliyan 200 akalla, na da mutum sama da dubu 16 da cutar ta kama, yayin kuma da ta yi sanadin wasu akalla 420, tun bayan bullarta a kasar cikin watan Fabrairu.

Hukumar da ke yaki da yaduwar annobar a kasar NCDC, ta ce sama da jami'an lafiya 800 ne suka kamu da larurar a yanzu.

Kungiyar likitocin da ke yajin aikin dai, ita ce ta wadanda ke neman kwarewar aiki, kungiyar da ke da 40% na adadin likitoci a Najeriyar.