1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rashin kayan aiki ya sanya likitocin Najeriya yajin aiki

April 1, 2021

Likitoci a Najeriya da ke aiki a asibitoci mallakin gwamnatocin jihohin kasar sun fara yajin aiki a wannan Alhamis.

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa da ake kira National Association of Resident Doctors a Turance Uyilawa Okhuaihesuyi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun fara yajin aiki bisa wasu alawus dinsu da suka makale a hannun gwamnati. Kazalika likitocin sun ce sun fantsama yajin aikin a sakamakon yadda rashin kayan aiki ke ci gaba da kawo cikas a asibitocin Najeriya.

Sai dai shugaban kungiyar likitocin ya ce duk da cewa a wannan safiya ta Alhamis suka fara yajin aikin, kungiyar likitocin za ta sake gudanar da wani taro a yau din nan domin ganin ko za ta janye yajin aikin biyo bayan tattaunawar da suka yi da bangaren gwamnati a ranar Laraba.