1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci sun yi zanga-zanga a Sudan

January 16, 2022

Gomman likitoci sun gudanar da zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan domin yin tir da hari da jami'an tsaro ke kai wa ma'aikatan kiwon lafiya a lokutan zanga-zanga a kasar.

Zanga-zanga a Sudan
Hoto: AFP/Getty Images

Likitocin da suka gudanar da zanga-zangar a wannan Lahadin na rike da hotunan abokan aikinsu da suka ce an kashe a rikice-rikicen da suka barke a kasar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban bara.

Guda daga cikin likitocin Haouda Ahmad ta baiyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, a lokutan da aka gudanar da zanga-zanga a kasar jami'an tsaro sun sha harba hayaki mai sa hawayen a asibitin da yake aiki.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da kai hari kan jami'an kiwo lafiya har sau 11 tun daga watan Nuwamban bara. Al'ummar kasar Sudan dai sun gudanar da jerin zanga-zanga a kasar don nuna adawa ga katsalandar da dakarun soji suke yi a sha'anin mulkin kasar.