1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci za su fara yajin aiki a Najeriya

September 5, 2020

Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati a Najeriya, za su fara wani yajin aiki, don neman karin albashi da kuma tilasta hukumomi su inganta musu yanayi na aiki.

Massenproteste in Nigeria
Hoto: dapd

Likitocin wadande ke rukunin masu neman kwarewar aiki ne da yawansu ya kai kashi 40% na likitocin kasar, za su fara yajin aikin ne daga makon gobe.

Matakin nasu kuwa na zuwa lokacin da Najeriyar da ta fi kowace kasa yawan al'uma a nahiyar Afirka ke fama da yaki da yaduwar cutar corona.

Majalisar koli ta kungiyar likitocin ta ce a ranar Litinin za su fara yajin aikin na kasa baki daya.

Yunkurin da suka ce ba makawa sai bukata ta biya, na neman gwamnatin kasar ta tabbatar musu Inshora ta iya rai.

Akwai ma batun biyan hakkokin wadanda ta Allah ta riske su a loakcin da suke kan aiki, a cewar shugaban kungiyar likitocin na kasa Dr. Aliyu Sokomba.