Lokacin mulkin mata yazo a Nahiyar Africa..
January 17, 2006Zambia......................
Shugabar adawa a kasar Zambia, wato Edith Nawakwi, tace da alama zata iya zamowa mace ta biyu da zata jagoranci wata kasa a nahiyar Africa.
A cewar Edith Nawakwi, hakan ya samo asali ne bisa kwarin giwa data dada samu a sakamakon rantsar da Ellen Jonhson Sirlef da akayi jiya, a matsayin shugabar kasar Liberia, wacce ta kasance mace ta farko da zata jagoranci shugabancin wata kasa a nahiyar Africa.
Edith Nawakwi yar shekaru 45, data taba rike mukamin ministar kudi ta kasar Zambia, a lokacin mulkin shugaba Chiluba, ta tabbatar da cewa lokaci yayi da mata zasu zage damtse a nahiyar Africa, wajen ganin ana damawa dasu yadda yakamata a harkokin mulki na kasashen su.
A cewar shugabar adawar ta jam´iyyar FDD,babban burin ta idan ta zamo shugabar kasar ta Zambia, shine inganta tattalin arziki, don kyautata rayuzwar talakawan kasar.