1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lugudan wutar NATO a harabar gidan Muammar Gaddafi

May 27, 2011

Nikolas Sarkozy ya sake jaddada bukatar Gaddafi yayi murabus daga shugabancin ƙasar Libiya.

Hoto: picture alliance/dpa

Jiragen yaƙi na gammaya a karƙashin jagorancin ƙungiyar tsaro ta NATO, sun sake kai sabbin hare-haren makamai masu linzami a babban birnin Libiya, watau Tripoli. Rahotanni na nuni da cewar a daren jiya an jiyo ƙarar saukar manyan makamai, tare da tashin hayaƙi a harabar gidan shugaba Muammar Gaddafi da sanyin safiyar yau. Tun a jiya ne dai dakarun dake biyayya ga shugaban na Libiya suka ƙaddamar da hare-hare a garin Misrata dake hannun 'yan tawayen ƙasar. NATO dai na ci-gaba da ƙoƙarin hamɓare gwamnatin Gaddafi, tun bayan da faɗan tawaye ya ɓarke a Libiyan, sama da watanni biyu dauka gabata. A taron ƙungiyar ƙasashe masu ci-gaban tattalin arziki ta G8 dake gudana a yankin arewacin ƙasar Faransa, shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya sake yin kira ga Muammar Gaddafi da yayi murabus daga kan muƙaminsa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal