Luguden wutar Isra'ila a Gaza
November 18, 2012Firayim ministan Isra'ila Benjamin Netenyahu, ya ce dakarun gwamnatinsa za su ci gaba da luguden wuta a zirin Gaza, har sai ƙungiyar Hamas ta daina cilla rokoki zuwa ƙasarsa.
Yau aka shiga kwana na biyar da ɓarkewar wannan saban faɗa tsakanin Isra'ila da Hamas, wanda ya zuwa yanzu,ya jawo asara rayuka kusan 70.
A wannan Lahadi kaɗai, sojojin Isra'ila sun hallaka Palestinawa kimanin 20, mafi yawan su mata da ƙananan yara a cikin hare-hare babu ƙaƙƙaftawa ta sararin samaniya.
A wani yunƙurin tsagaita wuta, ɓangarorin biyu sun shiga tattanawa a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, to saidai babu alamun cimma tundun dafawa, duk kuwa da kalamomin shugaban ƙasar Mohammad Mursi na fatan kaiwa ga masalaha.
"Cin ƙarfi,muna tuntuɓar ɓangarorin biyu, ta hanyoyi daban-daban domin dakatar da wannan fitina.Lale bamu da tabbas ko za mu cimma nasara, to amma dai muna cike da fatan hakan."
A halin yanzu dai abun na da kamar wuya, domin tuni ƙasar Isra'ila ta kimtsa shirin tura dakaru ta ƙasa zuwa zirin Gaza.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman