SiyasaArewacin Amurka
Lula zai gana da Kirchner ta Argentina da ke daurin talala
July 2, 2025
Talla
Lula na ziyarar ce a daidai lokacin da Kirchner ta fara zaman wakafi na daurin talalar shekara shida a gidanta da ke birnin Buenos Aires, sakamakon samunta da laifin cin hanci da rashawa.
Karin bayani: Christina Kirchner ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Argentina
A hukuncin da ta yanke a 2022, Kotun Kolin Argentina ta samu tsohuwar shugabar kasar da laifin zamba cikin aminci da rashawa. Hukuncin kotun ya kuma haramta mata rike mukaman siyasa har na tsawon rayuwarta.
Karin bayani: Olaf Scholz na Jamus zai gana da shugaban Argentina Milei
Kirchner, ta shugabanci Argentina a zangon mulki biyu daga 2007-2015, kuma tana daya daga cikin shugabannin kasar da suka yi farin jini, kafin ta fuskanci yankar kauna daga shugaba mai ci Javier Milei.