1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MƊD ta yaba da zaɓen majalisar dokoki a Masar

November 29, 2011

Ban Ki Moon ya yabawa Misirawa bisa juriyar da suka nuna wajen fafutukar tabbatar da dimoƙraɗiyya a ƙasashen Larabawa

Sakatare Janar na MƊD Ban Ki-MoonHoto: dapd

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yaba da nasarar da aka samu wajen gudanar da zaben majalisar dokokin ƙasar Masar cikin tsanaki da kwanciyar hankali, kana ya yaba da rawar da ƙasar ta taka wajen guguwar sauyin dake kaɗawa a ƙasashen Larabawa.

A cewar Martin Nesirky, kakakin babban sakataren, Mr. Ban Ki Moon ya yabawa Misiriwa da hukumomin Masar game da ɗokin da suka nuna wajen shiga a dama da su cikin shirin mayar da ƙasar bisa tafarkin Dimoƙraɗiyya, da kuma gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali.

Hakanan babban sakataren ya yabawa al'ummar ƙasar Masar bisa ƙudirin su na cimma dimoƙraɗiyya a ƙasar da kuma gudummowar da suka bayar wajen sake fasalin tsarin dimoƙraɗiyyar a yankin arewacin Afirka da kuma na Gabas Ta Tsakiya. Ban ya ce zaɓen daya gudana, wani muhimmin mataki ne wajen mayar da ƙasar bisa mulkin farar hula.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammed Nasir Awal