1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MƊD tace sojoji ne ke ruruta rikicin Siriya

May 24, 2012

A yayin da ake ci gaba da luguden wuta a Siriya MƊD ta zargi gwamnati da kawo cikas a yunƙurin kawo ƙarshen rikicin.

In this photo released by the Syrian official news agency SANA, a UN observer and Syrian army officer, left, listen to Syrian citizens during their visit to the pro-Syrian regime neighborhoods, in Homs province, central Syria, on Monday April 23, 2012. United Nations observers monitoring Syria's shaky cease-fire visited a string of rebellious Damascus suburbs Monday, while the European Union looked set to levy new sanctions to increase the pressure on President Bashar Assad's regime. (Foto:SANA/AP/dapd)
Jami'an MƊD a birnin HomsHoto: AP

A wannan Alhamis ce wata hukumar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙafa domin nazarin rigingimun Siriya ta zargi dakarun gwamnatin ƙasar da laifin galibin cin zarafin jama'ar dake ci gaba da wanzuwa a ƙasar, a dai dai lokacin da masu fafutuka ke cewar an sami rahotannin ƙaddamar da hare haren makamai akan yankin Bastion dake hannun 'yan tawaye. Hukumar, wadda mazaunin ta ke birnin Geneva ta ce galibin ta'asar da aka tafka tun bayan ɓarkewar rikicin na Siriya a cikin watan Maris na bara, jami'an tsaro da kuma sojojin gwamnati ne ke da alhakin afkawa yankunan da take ganin na masu adawa da ita ne.

A halin da ake ciki kuma shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ta Siriya wanda ya gana tare da ministan kula da harkokin yaɗa labarai da kuma sadarwar ƙasar Iran, Reza Taqipour, wanda ya kai ziyarar aiki a ƙasar ta Siriya, ya ce gwamnatin Siriyar ta san hanyar warware matsalolin da ƙasar sa ke fama dasu, kuma yana da ƙudirin tabbatar da dunƙulewar al'ummar ƙasar wuri guda. Furucin na shugaba Assad ya zo ne a dai dai lokascin da majalisar dokokin ƙasar ke zamanta na farko tun bayan gudanar da zaɓe. A wani ci gaban kuma, majalisar 'yan adawar ƙasar Siriya ta fara yunƙurin neman sabon shugaba, bayan da tsohon shugaban ta Burhan Ghalioun dake da mazauni a birnin Paris na ƙasar Faransa yayi murabus - a hukumance.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas