1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MƊD za ta yi zama akan Libiya

October 27, 2011

MƊD na shirin kawo ƙarshen izinin ɗaukar matakin sojin da ta bayar akan Libiya

Zaman kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: AP

A wannan Alhamis ce kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ke shirin gudanar da taro domin bada sanarwar kawo ƙarshen izinin da ta baiwa NATO na ɗaukar matakin soji akan ƙasar Libiya, matakin da kuma ya kaiga kifar da gwamnatin shugaba Gadhafi da ma kissar sa a cikin tsawon watanni bakwai da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta yi tana kai hare-hare ta jiragen sama akan ƙasar ta Libiya. Wannan matakin kawo ƙarshen izinin dai, yana zuwa ne duk kuwa da cewar majalisar wucin gadin dake tafiyar da lamura a ƙasar ta Libiya ta gabatar da buƙatar neman ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta jinkirta ɗaukar matakin tukuna - har sai ta gudanar da taron nazarin ko ya dace ƙungiyar ta tallafa mata samar da tsaro akan iyakokin ta. Idan har kwamitin sulhun - mai ƙasashe mambobi 15 ya amince da ƙudirin dokar neman kawo ƙarshen haramtawa jiragen sama yin shawagi ta sararin samaniyar Libiya da kuma baiwa dakarun ƙetare izinin shiga cikin ƙasar, to, kuwa ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO za ta dakatar da ayyukan ta a ranar 31 ga watan Oktobannan kenan. Ƙasar Birtaniya ce dai ta tsara ƙudirin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu