1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

M23 za ta janye mayakanta daga Uvira

Abdullahi Tanko Bala
December 16, 2025

Kungiyar 'yan tawayen M23 ta amince da bukatar Amurka na janye mayakanta daga birnin Uvira mai muhimmanci da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Mayakan 'yan tawayen M23 a garin Uvira a gabashin Kwango
Mayakan 'yan tawayen M23 a garin Uvira a gabashin KwangoHoto: Daniel Buuma/Getty Images

Kungiyar 'yan tawayen wadda ke samun goyon bayan kasar Rwanda a makon da ya gabata ta kwace birnin Uvira mai muhimmanci da ke kusa da kan iyakar Burundi 'yan kwanaki bayan da gwamnatocin Kwango da Ruwanda suka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu a Washington.

An dai sanya shakku akan yarjejeniyar sakamakon kutsen da 'yan tawayen na M23 suke kara yi wanda ya haifar da fargabar bazuwar yaki a fadin yankin.

Kungiyar ta ce za ta janye mayakanta don radin kanta ne bisa bukatar da masu shiga tsakani na Amurka suka yi mata a cewar wata sanarwa da da ta fitar

An shafe shekaru talatin ana dauki ba dadi a rikicin na gabashin Kwango mai arzikin ma'adanai.