1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ma'aikacin Reuters ya bace a harin Rasha a Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
August 25, 2024

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce guda daga cikin ma'aikatansa da ke Ukraine ya bace bayan wani mumunan harin Rasha da ya rutsa da 'yan jarida a gabashin kasar Ukraine.

Symbolbild Podcast Studio
Hoto: SeventyFour/Pond5 Images/IMAGO

Reuters ya ce wasu ma'aikatansa biyu sun sami raunuka a harin da ya same su a hotel din da suke.

Kazalika ko baya ga ma'aikatan na Reuters harin ya kuma jikkata wasu yan jarida biyu a garin Kramatorsk da ke gabashin Ukraine 

A cewar sanarwa da shugaban yankin Donetsk Vadym Filashikin ya fidda, yan jaridun sun fito ne daga kasashen Amurka da Birtaniya da kuma guda da yake dan asalin kasar. Akalla mutane 12 ne aka kashe a wannan harin.