Sabon kudin ‘yan fansho na Naira dubu 52,500 a Najeriya
November 11, 2026
Amincewa da sabon kudin fansho mafi kakanta ga wadanda suka yi ritaya wani gagarumin sauyi ne ga rayuwar ‘yan fansho a Najeriyar wanda baya ga kari daga aka samu na mafi kankanta kudin fansho na Naira 52,500. Sabon tsarin na yanzu ya bai wa dukkanin ma'aikacin gwamnatin da ya yi ritaya kuma yake cikin tsarin karbar Naira dubu 52,500 kowane wata a matsayin kudin fansho, maimakon tsari da a baya idan abin da ma'aikaci ya tara bai wuce kashI 1/3 na tsurara albashinsa ba, a kan biya shi kudinsa ne a jimlacebaya da fansho. Omolola Oloworaran it ace darakta janar ta hukumar fansho ta Najeriya da ta sanar da wannan sabon tsari da shugaban Najeriya ya amince da shi.
‘'daga yau kudin fansho ba zai zama kasa da Naira dubu 20 ba zai kasance Naira dubu 52, 500 sannan baya ga wannan akwai tsarin kula da lafiya dan fansho ko yar fansho za ta je asibiti ba wanda zai tambayeta wani kudi''
Tun a shekarar 2004 ne aka yi dokar da ta samar da wannan sabon tsari watau shekaru 22 kenan amma sai a wannan lokaci ne gwamnatin ta amince da aiwatar da shi, tare da bayyana cewa tsarin ya fara aiki daga ranar 10 ga watan Nuwamba shekara 2026 da aka amince da amfani da shi. Gwamnatocinda suka gabata sun yi biris da aiwatar da shi. Ko yaya ‘yan fansho suka ji da wannan kari? Umar Usman Toungo dan fansho ne a Najeriya.
Ma'aikatan gwanatin tarayya ne ke cikin wannan tsari na fanso inda suke bada gudumawar sannan gwamnati ta bada wani kaso. Musa Aminu ma'aikacin gwamnatin Najeriyar ne.
Sai dai kungiyar kwadagon Najeriya ta ce tana da ja a kan wannan kari da aka yi wa 'yan fansho a yanzu kamar yadda Comrade Nasiru Kabir sakatare tsare-tsare na kungiyarkwadagon Najeriya ta NLC ya bayyana.
Gwamnatin dai ta samar da Naira bikyan 400 don aiwatar da sabon tsarin da ya fara aiki, sannan akwai tsarin inshorar lafiya ga dukkanin dan fanshon da kudinsa basu wuce Naira dubu 150 ba. Masharhanta na fashin baki a kan bullo da tsarin a dai lokacin da gwamnati ke fusknatar zabe a badi