Ma'aikatan agajin da aka kashe a Afghanistan
August 9, 2010Wata ƙungiyar agaji ta fitar da jerin sunayen 'yan ƙetare takawas da 'yan bindiga daɗi suka kaiwa farmaki a arewacin ƙasar Afghanistan cikin makon jiya. Ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa - ta Christian Charity International ta tabbatar da cewar ma'aikatan agajin da suka gamu da ajalin su, sun haɗa da Bajamushe guda ɗaya, da ɗan ƙasar Birtaniya guda, kana da Amirkawa shidda.
A ranar jumma'ar da ta gabata ce jami'an 'yan Sanda a yankin da lamarin ya faru suka gano gawarwakin ma'aikatan waɗanda albarusai suka yi raga-raga da su. Ƙungiyar Taliban dai ta ɗauki alhakin kai harin bisa dalilin cewar, ma'aikatan agajin na yaɗa addinin kirista ne.
Sai dai darektan ƙungiyar agajin, Dirk Frans ya ce binciken su ya gano saɓanin hakan:
" Mun yi muhimman tambayoyi ga ɗaya daga cikin 'yan Afghanistan da suka tsira daga harin kuma ya shaida mana cewar sam-sam bai ga littattafan Bible ko kuma takardun adabi ba a tare da su."