1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ma'aikatan kamfanin kera motoci na Volkswagen na yajin aiki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 2, 2024

Kungiyar kwadagon kamfanin ta bukaci ma'aikatan su rufe duk wuraren aikin kera motocin da ke fadin Jamus, wanda shi ne kamfanin kera motoci mafi girma a fadin nahiyar Turai.

Ma'aikatan kamfanin kera motoci na Volkswagen
Hoto: Hauke-Christian Dittrich/dpa/picture alliance

A Litinin din nan ce ma'aikatan kamfanin kera motoci na Volkswagen ke fara wani yajin aiki mafi girma, don nuna kin amincewarsu da matakin kamfanin na rage albashi da kuma korar ma'aikata, inda suka kuduri aniyar garkame cibiyoyin kamfanin.

Karin bayani:Volkswagen zai sayar da reshensa na China

Kungiyar kwadagon kamfanin ta bukaci ma'aikatan su rufe duk wuraren aikin kera motocin da ke fadin Jamus, wanda shi ne kamfanin kera motoci mafi girma a fadin nahiyar Turai, domin nuna fushinsu kan matakan kamfanin na baya bayan nan.

Karin bayani:Volkswagen zai kori dubban ma'aikata

Kamfanin na Volkswagen ya bukaci ma'aikatan su amince da ragin kashi 10 cikin na albashinsu, wanda kungiyar kwadagon ta yi watsi da tayin, tare da neman tabbacin kare ma'aikata dubu dari da ashirin daga kora.