1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya na yajin aiki

Zulaiha Abubakar MNA
January 29, 2018

Makarantu da asibitoci da kuma cibiyoyin rarraba abinci a Zirin Gaza sun kasance a rufe a wannan Litinin sakamakon wani yajin aiki da ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a kasar ke yi.

Flash-Galerie Palästinenser Alltag in Gaza
Hoto: AP

Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a sassan makarantu da asibitoci da kuma cibiyoyin rarraba abinci a yankin Zirin Gaza na kasar Falasdinu sun kasance cikin yajin aiki na kwana guda. Ma'aikatan sun bayyana cewar matakin da Amirka ta dauka na datse agajin da take bayarwa wanda ake amfani da shi wajen gudanar da ayyukan taimako da suka shafi makarantu 278 a Gaza da dalibai dubu 300 suke halarta, shi ne ya fusata su suka yanke shawarar tsunduma cikin yajin aikin.

Sama da mutane miliyan biyu ne suka dogara da taimakon da suke samu daga bangaren aikin agaji na Majalisar Dinkin Duniyar da kuma sauran taimako da ke zuwa daga kungiyoyi masu zaman kansu, daidai lokacin al'ummar yankin ke fama da rashin ayyukan yi.