1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza ta ce Falasdinawa da Isra'ila ta halaka ya haura dubu 9

November 3, 2023

Hukumar lafiya ta duniya WHO za ta karbi marasa lafiya dubu goma sha biyar daga Gaza a kasar Masar don ba su kulawar gaggawa

Hoto: Abed Khaled/AP Photo/picture alliance

Ma'aikatar lafiyar yankin Zirin Gaza da ke karkashin ikon kungiyar Hamas ta ce adadin Falasdinawan da hare-haren Isra'ila suka hallaka ya kai 9,227, da suka hada da kananan yara 3,826 da kuma mata 2,405.

karin bayanAsibitoci da dama sun rufe a Zirin Gazai:

A gefe guda kuma babban jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO a kasar Masar Ahmed Al-Mandhari, ya shaidawa DW cewa tuni suka yi nisa wajen karbar marasa lafiya dubu goma sha biyar daga Gaza, don ba su kulawar gaggawa.

Karin bayani:Guterres ya bayyana damuwa kan kisan mutane a Gaza

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban jiya ne dai sabon rikicin Isra'ila da Falasdinawa ya sake barkewa, bayan da kungiyar Hamas ta harba rokoki zuwa Isra'ila, wanda ya hallaka 'yan Isra'ila dubu daya da dari hudu, inda ita kuma ta ke ci gaba da mayar da martani har yanzu.