1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kama ma'aurata saboda rawa

Abdul-raheem Hassan
February 1, 2023

Ma'auratan biyu za su shafe shekaru 10 a gidan yari, bayan da kotun musulunci ta same su da laifin wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta suna rawa kuma amaryar ba ta yi lullubi ba.

Ma'auratan da aka daure kan yin rawaHoto: UGC/AFP

Wata kungiyar kare hakkin jama'a ta Amirka, ta ce tun a watan Nuwamban 2022 aka kama ma'auratan Amir Mohammad Ahmadi mai shekaru 22 da Amaryarsa Astiyazh Haghighi mai shekaru21 bisa zargin saba dokokin shari'a na yin rawa babu lullubi a bainar jama'a.

Tun a tsakiyar watan Satumban shekara ta 2022, matasa na ta gudanar da zanga-zangar adawa da tsauraran dokokin gwamnati a Iran, bayan mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini a hannun 'yan sanda bayan da aka tsare ta kan saba ka'idar sa sutura ta addini.