1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara yi wa mace rigakafin corona a duniya

December 8, 2020

Murna ta kaure a wani asibitin Birtaniya a lokacin da Margaret Keenan mai shekaru 90 dai haihuwa ta fara karbar rigakafin corona a duniya.

England | Coronavirus | erste landesweite Impfungen
Hoto: Jacob King/AP Photo/picture alliance

Margaret Keenan ta ce allurar rigakafin corona ta zama tamkar wata babbar kyauta a gare ta a lokacin da take gab da shiga shekaru 91. Rahotanni sun bayyana cewa sarauniyar Ingila Elizabeth II da ke da shekaru 94 da haihuwa na daga cikin rukunin farko da za a yi wa rigakafin saboda yawan shekarunta.

Kasar Birtanya ta tanadi allurar guda miliyan 40 don yi wa mutane miliyan 20 a rukunin farko na rigakafin. Kasar ta shiga wani wadi na tsaka mai wuya sanadiyar annobar corona da ta yi mata illa fiye da kowace kasa a nahiyar Turai inda cutar ta kama mutum kimanin miliyan daya da rabi.